An Gama Binne Gawar Khadimur -Ridha shahid shugaban kasar Iran a hubbaren Imam Rida (a.s) da fa ke birnin birnin Mashhad
Ana Gama Ta Rufe Shahid Ayatullah Ibrahim Raisi Shugaban Kasar Iran ruwan sama na sauka a birnin Mashhad.
Akwai sallah da ake gabatarwa a daren da aka binne mamaki raka'a biyu ce. Takarar farko Fatiha da Ayatul Kursiyyu. Raka'a ta biyu bayan Fatiha ana karanta Suratu Inna Anzal nahu kafa goma. Bayan sallama sai ayi salatin Annabi Muhammad Sawa sannan ayi kyautar sallah din ga mamacin da akai dominsa. Za'a iya yi da nufin dukkanin Shahidan sai a ambaci sunayensu a karshen salla ɗin ajere kamar haka:
1- Sayyid IBrahim Raisi Bin Sayyid Haji
2- Husain Amir Abdullahiyan Bin Muhammad
3- Sayyid Muhammad Ali AlHashim Bin Sayyid Muhammad Takiy.
4- Malik Rahmaty Bin Iskandar.
5- Sayyid Ɗahir Musdafawy Bin Sayyid Ahmad.
6- Muhsin Daryanush Bin Muktar.
7- Bahroz Qadimy Bin Is'haq
Daren Gobe:
8- Sayyid Mahdy Bin Sayyid Muhammad Ali
Alura: wannan sallar kamata yayi ayiwa kowa tashi ɗaya bayan ɗaya amma bisa lalura idan bai yiwu ba za'a iya yin kwara ɗaya da niyyar dukkansu amma in an gama sallah sai a ambaci sunayensu gaba daya.
Alura: Mutum na ƙarshe na takwas kenan sai gobe juma'a za'a binne shi don haka shi sai gobe za'a masa ta sa Insha Allahu.
Alura: wannan salla ɗin tana da matukar muhimmanci ga wanda yayi da wanda akai ta dominsa. Akwai lada mai dinbin yawa wanda malaman hadisai suka ruwaito mai bukata zai iya bincikar sunan ta domin samun karin bayani (Salatul Wah'shah= صلاة الوحشة )
Anan kasa akwai hoton bayanan yadda ake yinta a takaice a cikin hoton nan:

